Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dare teburin Firimiya lig 2016/2017 Mako Na Goma Sha Biyu


Sakamakon ya kasance na mako goma sha biyu Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi kunnen doki 1-1 da Arsenal

Southampton tayi canjaras 0-0 da Liverpool

Crystal Palace 1-2 Manchester City

Watford na da 2 Leicester City na da 1

Everton ta yi 1-1 tsakaninta da Swansea city

Stoke tasha kashi a hannun AFC Bournemouth da ci 1-0

Sunderland ta lallasa Hull City da kwallaye 3-0

Tottenham ta doke Westham daci 3-2

MiddleBrough tasha kashi a hannun Chelsea da ci 1-0

Yau kuma za'a kece raini tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Westbromwich da Burnley da misalin karfe tara na dare agogon najeriya Nijar da kuma kamaru.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu nasarar darewa kan ragamar teburin firimiya lig sakamakon nasarar da ta samu a wasan da tayi da MiddleBrough

A yanzu haka Chelsea na mataki na daya da maki 28, sai Liverpool a mataki na biyu da maki 27, Manchester City na mataki na uku da maki 27.

Kasan teburin kuwa Hull City na mataki na goma sha takwas da maki 10, Sunderland na mataki na sha tara da maki 8, Ita kuwa Swansea city na mataki na A.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG