Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, na shirye shiryen ganin cewa sun sawo dan wasan gaba na Liverpool, mai suna Daniel Sturridge, a watan Janairu mai zuwa da zaran anbude hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa.

Tsohon dan wasan kasar Italiya Andrea Pirlo, ya ce yayi dana sanin rashin bugawa Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ko Barcelona.

Pirlo mai shekaru talatin da bakwai da haihuwa a yanzu haka yana Kungiyar kwallon kafa ta New York City dake kasar Amurka tun shekara 2015 da yabar AC Milan.

Isco na Real Madrid, yaki amincewa da tayin da kungiyar ta masa na sabunta kwanteraginsa.

Manchester United, na zawarcin dan wasan baya na Napoli mai suna Elseid mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa.

Ita kuwa Chelsea, a nata bangare, tasa yuro miliyan €4 domin sayan maitsaron ragar AC Milan mai suna Donnarumma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG