Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idon Cristiano Ronaldo Yana Kan Kambin Ballon d' Or Na Bana


Bayan lashe kofin zakaru na bana Cristiano Ronaldo, ya aiyana cewa kakar wasan ta bana itace kakar da yafi yin ta gomashi.

Har ila yau dan wasan ya ce idonsa na kan mashahurin kyautar nan ta kambin Ballon d’Or, na bana, yana mai cewa ya cancanci ya lashe kambin.

Ronaldo, mai shekaru talatin da daya, yana cikin jerin sunayen wadanda ake sa ran cewa suna iya lashe wannan kambi, na dan wasan da yafi kowane dan wasan taka leda a duniya.

Cristiano Ronaldo, ya jefawa Real Madrid, kwallaye hamsin da daya a cikin raga a wasani arba’in da takwas a kakar data gabata ya kuma ci kwallaye goma sha shida a wasani goma sha biyu. Real Madrid, ta lashe kyautar sau biyu a cikin shekaru ukku.

Ronaldo, wanda ya sha suka a wasu wasanin da suka buga na rashin tabuka abin a zo a ganin ya samu nasarar dabarar cin kwallaye ukku, a wasan da suka buga da kishiyarsu Atletico Madrid.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00

XS
SM
MD
LG