Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Cigaba Da Wasannin Lig Lig 2016/2017 Mako Na Goma Sha Biyu


A yau jumma'a 18/11/2016 za'a cigaba da fafatawa a wasannin lig lig na kasashe daban daban kama daga La-liga ta kasar Spain da firimiya ta Ingila da dai sauransu na shekarar 2016/2017 sati na 12.

A bangaren La-liga Kungiyar kwallon kafa ta Real Betis za su kece raini da Las Palmas da misalin karfe tara saura kwata agogon Najeriya Nijar da kamaru.

Gobe kuwa Deportivo zata kara da Sevilla

Barcelona zata karbi bakuncin Malaga

Eibar da Celta vigo

A goben za'a buga babban wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da Real Madrid

Yayinda a bangaren firimiya ta kasar Ingila, a gobe a kwai kece raini tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da takwararta Arsenal, da misalin karfe daya da rabi na rana agogon najeriya Nijar da kamaru.

Southampton da Liverpool

Crystal Palace zata kara da Man City

Watford da Leicester City

Stoke city zata karbi bakuncin AFC Bournemo

Everton da Swansea

Sunderland da Hull City

Tottenham da Westham.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG