Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Flying Flamingo Old Stars Bauchi Zasu fafata a wasan ADC Gwamnan Bauchi


Flying Flamingo
Flying Flamingo

Tsohowar Kungiyar kwallon kafa ta Flying Flamingo dake cikin garin Bauchi zasu kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Bakari Old Starts suma na garin Bauchi a gasar cin kofin Dogarin gwamnan Bauchi SP ADO karo na biyu.

Kungiyar Flamingo ta kunshi manya manyan tsofaffin 'yan wasan kwallon kafa da suka yi suna a Najeriya irin su Pascal Patrick, tsohon dan wasan Super Eagles, wanda ya halarci gasar Olympic a kasar Amurka a shekara ta 1996 da Ibrahim Umar, da Ya buga wa Golden Eaglet a Shekara 1994

Sauran 'yan wasan da zasu fafata a wasan sun hada da Tsohon kaftin na Wikki Tourist, Yakubu Yankari, da Iliya Arrow, da Ahmad Captain, wanda ya buga wa Kungiyar kwallon kafa ta CBN, a shekarun baya da kuma Shehu Adamu, na kwalejin Tatari Ali, dake cikin garin Bauchi.

Har ila yau akwai wasu manya manyan 'yan wasan kwallon kafa da suka shahara a fagen tamola shekarun baya.

Za'ayi wasanne Gobe Jumma'a 18/11/2016 da misalin karfe 4:00 na yamma a filin kwallon kobi, dake cikin garin Bauchi, inda ake sa ran manyan baki daga bangaren Gwamnati zuwa masoya kwallon kafa a fadin kasannan baki daya.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG