Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Bukaci Kotu Ta Amsar Masa Kudin Da Ya Kashe Bayan Matar Sa Ta Yi Batan Dabo Sati Biyu Bayan Aure


Wani mutum mai suna Mr Echele ya bukaci kotu ta amsar mashi zunzurutun kudi Naira dubu dari biyu daga tsohuwar matarsa mai suna Gloria, a dalilin cewa makonni biyu kacal ya ci moriyarta.

Mujallar Daily Trust ta wallafa cewa Mr Ideh ya kai kukansa ne gaban kotu a jihar Nasarawa bayan matarsa ta arce ta barshi sati biyu bayan an daura masu aure.

Mutumin ya bayyanawa kotun cewa an daura masu aure a shekarar 2013, ne bayan sati biyu da daura auren matar ta yi batan dabo.

Ya kara da cewa bayan wasu kananan bukatu, ya saw a mahaifanta kudi Naira 300,000, da kuma Naira 70,000 a asusun ajiyarsu na banki kamar yadda suka bukata a al’adance. Ya kuma biya kudi Naira 199,000 domin jigilar duka iyalin zuwa kauyen matar mai suna Isi Ala Ngwa, dake jihar Abia.

Bayan wannatni da daman a bacewarta , kwatsam sai ta kira shi a waya inda ta bayyana masa cewa ta sake wani auren, ya ce ya bayyanawa iyayenta abinda ya faru amma babu abinda suke masa sai barazana, cewar duk yadda zai yi ya nemo masu daiyarsu.

Ya ce yana bukatar a biya shi kudi Naira dubu dari biyu N200,000, akan bata lokacin nemanta da yayi da kuma tashin hankalin data sa shi ciki, bugu da kari har ya nuna shaida akan kudin da ya kashe, koda shike Mr Anayo mahaifin matar ya ce atafau bai yarda da kudin da sirikin nasa ya ce ya kashe ba, a mamakon haka shidai yasan dubu dari kadai ya kashe kamar yadda al’ada ta bukata.

Mai shari’a Albert Maga, y adage sauraren karar sai nan gaba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG