Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

The Rock Ya Bayyana Ra'ayin Sa Na Fitowa Takarar Shugabacin Amurka 2020


Shahararren dan wasan kokawar nan na kasar Amurka mai suna Dwayne Johnson, wanda aka fi sani da The Rock, ya fito ya bayyana ra’ayinsa na fitowa takarar shugabancin Amurka a shekarar 2020.

A hirar su da Vanity Fair Magazine, The Rock ya ce bai fitar da ran zama shugaban kasar Amurka bayan zababben shugaban kasar mai jiran gado na yanzu Donald Trump.

Dan wasan kokawar mai shekaru 44 da haihuwa ya bayyana ra’ayin nasa ne kwananki kadan bayan dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Repulican Donald Trump, ya lashe zaben kasar inda ya zamo shugaban Amurka na 45, The Rock ya ce yayi imanin samun goyon bayan jama’a a matsayinsa na dan kasa daga wurin sauran jama’a.

Ya kara da cewa taimakawa al’umma abin alfahari ne, kuma me yiwuwa, domin wannan zaben da ya gabata ya nuna cewar komai na iya faruwa.

The Rock ya kara da cewa bai fidda ran zama gwamna ko shugaban kasa watarana ba, kuma dama ce ta taimakawa jama’a dan haka ya ce idan da rabo watarana akori kurarsa zata sami wurin parking a fadar White House.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG