Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Babu Komai Na Dawo Da Martabar Harshen Hausa - Inji Asma’u Sadiq Mai Wakar Gaɗa


Asma’u Sadiq Mai Wakar Gaɗa
Asma’u Sadiq Mai Wakar Gaɗa

Mama gaɗa wacce ta koma wokikin gaɗa da zumar dawo da martabar hashen Hausa, mussamam ma da ta lura da cewar al’adun malam bahasuhe na neman gushwewa.

Asma’u Sadiq , wacce aka fi sani da Baby nice ko mama gaɗa ta ce a yanzu ta fi maida hankali a wakokin gaɗa ne a wuraren bukukuwa da sauran taruka na matasa maimakon raya al’adu wasu kabilun .

Ta ce alal misali irin yadda ake yi a da, kamar zaman dandali da gaɗa, matasa a yanzu sun fi raja’a ne wajen kawikwayon wasu al’adun mafi yawa na Indiya ko Arabian night hakanne ya sa ta kafa dandalin gada a bukukuwa da ma wasu taruka.

Matashiyar ta ce kimanin shekaru biyar Kenan da ta sauya sheka daga wakokin soyayya da na ‘yan fim zuwa ga wakokin gada, kuma tun daga lokacin da ta fara gaɗa ta samu natsuwa a cewarta ko ba komai ta dawo da martabar harshe.

Asma’u Sadiq, mama gaɗa, ta ce suna gudanar da harkar gaɗarsu cikin tsafta da tsari .

A fannin mu na tsegumi kuwa fitattacen dan wasan barkwancin nan Seyi Law a shafinsa na twitter ya bayyana cewar nan da shekaru uku masu zuwa zai tsaya dan takarar shugabancin Nigeria, a cewarsa masu iya Magana na cewa idan zaka roka toh ka roka da baban masaki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG