Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Daga Baya Ta Gane Yana Da Mata Da 'Ya'Ya 6


Wata mata mai suna Lydia Dalla, ta bayyanawa kotun majistire dake Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja cewar mijinta ya yaudareta ta dalilin kin shaida mata yana mata da ‘ya’ya shidda kafin ya aureta.

Yayinda ta bukaci kotu ta raba auren, Lydia ta bayyana wa kotu cewar ta gano cewar mai gidan nata wanda aka bayyana sunan sa Yakubu Dalla, ya taba aure har yana da ‘ya’ya bakwai bayan ta kunla alkawarin aure da shi.

A cewarta, mijin nata bai taba fada mata ya taba yin aure har yana da ‘ya’ya guda bakwai ba., sai bayan an daura auren kana ta gano cewar ya taba yin aure har yana da yara bakwai, ta kuma kara da cewa a duk lokacin data nemi ya bar ta domin ta tafi, sai yayi barazanar hallakata.

Lydia ta kara da cewa harma ya farfasa wasu daga cikin kayan dakinta, inda makwabta suka kawo mata dauki, matar ta bayyana cewa bayan ta gane cewar yana da aure ta tunkare shi da maganar sai kawai ya kamata da duka fanka, da makwabata suka ji tana neman dauku ne suka yi tururuwa cikin gidan har suka kwace ta.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa daga baya Lydia ta je wani dakin shan magani inda ta bayyana abinda ya faru da ita, kafin ;yan sanda suka gaiyace shi zuwa afishinsu.

Daga karshe ta nemi kotu ta raba auren tare da bata ‘ya’yanta duk da cewa mai gidan nata ya karyata zargin da ake yi masa

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG