Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kashe Dan Abokinsa Domin Yayi Tsafi Dashi


Rundunar ‘yan Sandan jihar Nasarawa, ta cafke wani mutun mai suna Emmanuel Ishaya, mazaunin kauyen Ushata da ke jihar Nasaraw a bisa zargin kashe dan abokinsa Isaac Joshua, mai shekaru bakwai domin yin tsafi

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Idrissu Kenedy, yace an damke wanda ake zargin ne bayan da mahaifin yaron Mr. Joshua Ebini, ya kai rahotun ga ‘yan Sanda cewa dansa ya bata.

Kakakin yace Mr. Emmanuel Ishaya , ya fada masu cewa ya yaudari yaron ne inda ya goya shi akan babur zuwa wani daji inda ya kashe yaron ya kuma yanke mazakutan yaron da wasu sassan jikinsa kamar yadda abokan cin mushensa suka umarce shi.

Kakakin ya ce bayanan da wanda ake zargin watau Emmanuel Ishaya, ya baiwa rundunar ‘yan Sandan ya taimakawa rundunar wajen cafke wasu mutane ukku, inda kuma ana ci gaba da neman na hudun su.

XS
SM
MD
LG