Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi Ya Wuce Cristiano Wajen Lashe Kyaututtuka


An zabi Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa wanda yafi kowane dan wasa lashe kyaututtuka a bangaren kwallon kafa a duniya a shekaru goma da suka wuce wanda kamfanin jarida na (Goal 50 ) ya bayar a bana inda Cristiano Ronaldo na Real Madrid yake mataki na biyu.

Andres Iniesta, shike mataki na uku yayin da zlatan Ibrahimovic, na Sweden, yake biye masa a mataki na hudu.

Sauran sun hada da mai tsaron baya na Real Madrid, Sergio Ramos, a matsayi na biyar sai tsohon dan wasan Barcelona, Xabi, amatsayin na shidda, Nermar, na mataki na bakwai Arjen Robben, na Bayern Munich, ke mataki na Takwas Thomas Muller, kuma na mataki naTara Shi kuma Luis Suarez, yana mataki na Goma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG