Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester City Ta Fara Zawarcin Lionel Messi


Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, na zawarcin Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina maitaka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma zakaran kwallon kafa na duniya Lionel Messi.
Manchester City, ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £200 domin sayen dan wasan inda zata kuma biyansa fam dubu dari £500 a duk sati in haka ya tabbata Messi zai zama dan wasan da yafi kowa tsada a duniyar tamola.
A satin da ya gabata ne dai Kungiyar sa ta Barcelona ta nuna sha'awarta na cewa Messi, ya sake rattaba hannun domin ci gaaba da zama a kulob din sai dai Messi, ya neme da a bashi lokaci ba yanzuba domin akwai sauran lokaci a kwanteragi sa har na tsawon shekaru biyu masu zuwa inda zai kammala a shekarar 2018.
Kungiyar ta Barcelona na ganin indai bai amince ya sake rattaba hannun ba to ya zamo dole su sai dashi a shekara mai zuwa in ba haka ba zai iya tafiya wata kulob kyauta wato (Free Transfer ) sai dai har yanzu ba'aji ta bakin dan wasan ba game da tayin da kungiyar ta Manchester City tayi masa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

XS
SM
MD
LG