Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Kwallon Kafa Na Duniya


A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta saka zunzurutun kudi har Yuro miliyan €50 domin sayen mai horas da kungiyar kwallon kafa na Atletico Madrid mai suna Diego Simeon.

Manchester United, na zawarcin dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, mai shekaru ashirin da uku da haihuwa.
Har kuma kungiyar ta Manchester, na yunkurin sawo dan wasan gaba daga Kungiyar kwallon kafa ta Juventus, mai suna Paulo Dybala.

Arsenal da Liverpool na takara wajan zawarcin dan wasan mai suna Andrea Belotti daga Kungiyar Torino.

Yayinda Westham ta saka fam miliyan £25 don sayan dan wasan Liverpool mai suna Daniel Sturridge.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus, da Manchester City, na zawarcin Alex Sanchez, PSG ta saka yuro miliyan £20 domin zawarcin dan wasan Santo Thiago Maia.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG