Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitattun Labaran Wasanni


Kungiyar Real Madrid ta sake komawa kan batun sayen mai tsaron raga na Manchester United David de Gea tare da dan wasan tsakiya na kungiyar dan kasar Faransa Paul Pgoba, da kuma Anthony Martial.

Har ila yau Kungiyar ta Real madrid tana son ganin ta dauko dan wasan gaba na Liverpool Mohammad Salah da Harry Kane daga Tottenham tare da Robert Lewandowski, na kungiyar Bayern Munich.

Dan wasan tsakiya na Monaco Fabinho ya bukaci barin kungiyar don koma wa Firimiya lig ta Ingila inda Manchester united, ta nuna sha'awarta kan dan wasan.

Liverpool tana duba yuwuwar dauko dan wasan gefe na Gent Moses Simon, wanda kungiyoyin Newcastle, da Brighton suke zawarcin sa.

Dan wasan tsakiya na Manchester united, Andreas Pereira, zai tattauna da Kocin kungiyar kafin ya san makomarsa a kulob din, dan wasan dai yanzu haka yana fafatawa a Valencia, a matsayin aro.

Da yuwuwar kungiyar Chelsea, zata dauko Kocin Juventus Massimiliano Allegri ko Kocin Monaco, a matsayin kocinta wanda daya daga cikinsu zai maye gurbin Antonio Conte, bayan da ta kasa cimma yarjejeniya da tsohon Kocin Barcelona Luis Enrique.

Ita kuwa Real Sociedad, tana duba yuwuwar dauko Kocin Newcastle ne Rafael Benitez, da ya dawo gida a matsayin sabon Kocin kungiyar wanda shima zai maye gurbin kocinta mai ci a yanzu.

Chelsea, ta fice daga zawarcin mai tsaron raga dan turkiya mai suna Berke Ozer, wanda yake wasansa a kungiyar Altinordu. Manchester City ta sanya wata yarjejeniyar shiga zawarcin matashin dan wasan Barcelona mai shekaru 15 mai suna Robert Navarro, har yanzu Barcelona bata bada dama kan dan wasanba.

Kungiyar Westham, ta ce zata cigaba da tafiya da Kocinta David Moyes a matsayin sa na Kocin kulob din, bayan da ya tallafa wa kungiyar ta haye daga fadawa Relagetion.

Dan wasan tsakiya na Newcastle Mikel Merino, ya shaida wa kungiyar cewar zai bar kungiyar dan komawa gasar Laliga a kulob din Athletico Bilbao.

Leicester city da Bournemouth da kuma Aston Vila sun shiga sahu guda domin duba yuwuwar dauko dan wasan gaba na Southampton mai suna Charlie Austin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG