Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Ke Wakana A Duniyar Tamaula


Kocin Kungiyar kwallon Kafa ta Stoke city Paul Lambert ya bukaci a yi amfani da Mataimakin alkalin wasa na na'urar bidiyo (VAR) a wasan Firimiya lig na kasar Ingila, Kocin ya fadi hakanne bayan an tashi a wasansu da Arsenal a gasar Firimiya lig mako na 32, inda aka Arsenal bugun daga kai sai mai tsaron gida har guda biyu a wasan, an kuma tashi Arsenal tana da ci 3-0.

Shi kuwa dan wasan gaba na Monaco, Radamel Falcao, ya,ce kwata kwata bai kamata ake amfani da (VAR) ba domin zata iya kashe wa mutune kwarin gwiwa, shima ya fadi hakanne sakamakon bugun da ya sha a hannun PSG a wasan karshe na Coup de LA lig 3-0.

Dan wasan tsakiya na Manchester, united Paul Pgoba, ya ce shi baya da wata matsala da Kocin kungiyar José Mourinho, kuma baya tunanin cewar zai bar kulob din a yanzu duk da cewar baya samun kansa a wasu wasanni da Manchester take bugawa, sai dai Kocin ya ce shi yasan dalilin sa na ajiyie dan wasan a waje amma ya san yadda zai gyara abinsa.

Kungiyoyin Everton, Westham da Swansea, suna zawarcin dan wasan gaba na kasar Mali, mai taka leda a kungiyar FC Porto mai suna Moussa Marega 26,

Dan wasan baya na Barcelona, Samuel Umtiti, ya ce yana jin dadin zaman sa a kungiyar ta Barcelona, duk da kasancewar Manchester united ta nuna sha'awarta ta ganin ta dauko dan wasan dan kasar faransa mai shekaru 24.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:14 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG