Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Da Suka Taka Rawar Gani A Gasar Badminton Easter Fiesta A Jihar Bauchi


An fara gasar cin Kofi na wasan Badminton karo na biyu mai taken Easter Fiesta 2018, a jihar Bauchi dake tarayyar Najeriya, Wadda kungiyar Bauchi Multipurpose Badminton Club, ta ke daukar nauyi duk shekara inda kungiyoyin wasan Badminton daga jihohi goma sha biyar suka halarta wanda ya hada da birnin tarraya Abuja.

Ita dai wannan gasa ana yin ta ne bisa tsarin tsofaffi ‘yan wasan wato (Veterans) sai dai a bana an sake tsari. Akwai sahun yara ‘yan kasa da shekara 14 da kuma na manyan ‘yan wasa sai na tsofaffi.

A jiya aka buga wasan karshe na ‘yan kasa da shekaru 14 inda aka kara tsakanin Umar Shamsuddeen daga Golden Star Club, Katsina da kuma Usman Umar, daga Multipurpose Club Bauchi.

Umar Shamsuddeen, daga Katsina shi ya lashe lambar Zinare, Usman daga Bauchi kuma ya zo na biyu ya lashe Azurfa. Sai wanda suka lashe Tagulla Sadam Ahmed, da Kamilu Muh'd duk kansu daga Multipurpose club Bauchi.

Babban bako a wajan wadda ya mika kyauta ga yaran da suka samu nasara shine Mai Martaba Sarkin Gashua, Alh Abubakar Ibn Umar Suleman Mai Bade.

A bangaren wasan manya kuwa ana matakin wasan dab da na karshe ne Semi Final inda Ahmed Balarabe Umar daga Multipurpose Club Bauchi, zai kara da Sunday Musa daga Taraba. Sai kuma Mujitapha Umar daga Multipurpose Club Bauchi, zasu fafata da Mustapha Moh'd daga (Friendship) Kaduna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG