Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Hukumar NFF Ta Ziyarci Carl Ikeme


Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tura tawaga mai karfi don kai ziyara ga mai tsaron ragar Super Eagles, Carl Ikeme, a asibiti a ranar Litinin, yayin da kungiyar ta Super Eagles, ke shirye shiryen wasan sada zumunta da Serbia a London, shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, ya jagoranci tawagar ' NFF don ziyartar Ikeme a asibitin Christie a Manchester, inda ake masa jinya sakamakon cutar Sankarar bargo,

Pinnick ya ce: "Mun zo ne a madadin gwamnatin Najeriya da hukumar NFF don duba lafiyarka kuma mu sanar da kai cewa har yanzu kana cikin zukatanmu da kuma mamba na Super Eagles ta Nijeriya.

Ikeme, ya kasance mai tsaron raga na kungiyar Super Eagles, na farko da aka zaba kafin gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekara ta 2018, inda ya kama wasan da Najeriya ta yi da Swaziland, da kuma wasan farko na rukunin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Zambia a Ndola.

Amma watanni tara da suka wuce, aka gano cewa yana dauke da cutar sankara bayan anyi "gwajin jini" a lokacin gwaje gwajen farko a kungiyarsa ta Wolverhampton Wanderers, a Ingila.

Hukumar ta NFF ta karrama dan wasan inda ta bashi gayyata ta musamman a matsayin babban bako a wasan da Najeriya zata yi da kasar Ingila a wata mai kamawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:45 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG