Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Yiwa 'Yan Wasan Commonwealth Alkawari


Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta yi alkawarin bai wa duk 'dan wasanta da ya samu nasarar lashe lambar zinare a gasar Commonwealth da ake yi ta shekarar 2018, a kasar Australia da tukuicin kudi har dalar Amurka dubu $ 5,000. ga duk wanda ya lashe lambar Zinare.

Ministan wasanni Mr Solomon Dalung, wanda ya bayyana kyautar kudi ga 'yan wasa 90 da ke wakilci kasar a wasannin karo 21 na Commonwealth, wanda aka bude a Australiya birni na shida mafi girma a ranar Laraba,

Ya kuma bayyana cewar duk dan wasan da ya ciwo azurfa zai karbi dala dubu $3,000, Masu tagulla kuwa za'a basu dala dubu$ 2,000, kowannen su bisa kukarin da suka yi.

A shekara 2014 Najeriya, ta samu nasarar lashe

Zinare 11

Azurfa 11

Tagulla 14

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yayi kira ga ‘yan wasan da suke wakiltar Najeriya, a gasar da su zamo wakilai na gari ya kuma bukace su da su zage damtse domin samun nasarar ciwo lambobin yabo fiye da na shekarun da suka wuce, ya yi masu fatan alheri a yayin da suke kasar ta Australiya, ‘yan wasa dubu 6, 600 ne zasu fafata a wasan daban daban daga kasashe 71.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG