Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasan Badminton Na Jihar Bauchi


A ranar asabar 31/3/2018 aka kammala wasannin Badminton, wanda akai masa lakani da (Easter Feista 2018) karo na biyu a jihar Bauchi a tarayyar Najeriya, wadda kungiyar Bauchi Multipurpose Badminton Club take daukar nauyi duk shekara domin farfado da wasan da kuma tunawa da tsofaffin ‘yan wasan badminton da suke wasu jihohi a fadin Najeriya.

A bana, jihohi goma sha biyar ne suka halarci gasar wadda ta hada da babban birnin tarayya Abuja, a ranar rufewar an buga wasannin karshe bisa mataki mataki Kamar haka:

Matasa masu Motsi a yanzu (Active) Wanda ya lashe zinare shene

1. Mustapha mohammed friendship bc kaduna Azurfa

2. Ahmad B. Umar, Mpbc,Bauchi Tagulla

3. Mujitapha Umar Mpbc, Bauchi

3. Sunday Musa Taraba bc

Sai bangaren mata su biyu biyu (Women's doubles) Zinare

  1. Lola da endurance citygate bc,Abuja, Azurfa

2. Tolu da Esther Mpbc, Bauchi, Tagulla

3. Sidiqat da Annie Zuma Bc, Suleja

  1. queen da Caro, ABU Bc, zaria

A bangaren Maza yan sama da shekaru 35-49 ( Double) Zinare

1. Baba da hayatu, exclusive bc, kaduna, Azurfa

2. Hayatu da uwaisu Mpbc, Bauchi, Tagulla

3. Haruna da hayatu Gombe Bc

3. Sani da Musa, zuma BC, Suleja

Sai tsofaffi wada suka dara shekaru 50 (double) zinare

1. Musa da Bashir, Damaturu bc, Azurfa

2. Ibrahim da danlami, IBB veterans, minna, Tagulla

3. Sunoma da Mamza, Kanem BC, Maiduguri

3. Gamji da Maina, DSBC, Gashua

Babban bako da ya mika kyauta a wajan shine Mai martaba Sarkin Gashua Alh Abubakar Ibn Umar Suleman (Mai Bade).

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG