Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pochettino Ya Ce Jagorancin Sa A Real Madrid "Da Muguwar Rawa Gara Kin Tashi"


Kungiyar kwallon Kafa ta Swansea City, tana shirin bayyana sunan Graham Potter dan kasar Ingila mai shekaru 43 da haihuwa a matsayin sabon kocinta tare da Mataimakin sa Billy Reid,

Graham da Billy, zasu yi aiki tare don maye gurbin tsohon kocinta Carlos Carvalhal, wanda ya bar aikinsa bayan da ya Kai kungiyar (Relegation) wato gasar kasa ta Firimiya lig ta kasar Ingila.

Kocin kungiyar kwallon Kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino, yayi watsi da damarsa ta kasancewa Sabon Kocin kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid, wacce ta yi masa tayin maye mata gurbin tsohon kocinta Zinedine Zidane, wanda ya ajiye aikinsa a kungiyar bayan ya shafe shekaru biyu da rabi a matsayin mai horaswa.

Pochettino, ya ce babban dalilin sa na kin amincewar shine yana shakka idan kungiyar zata bar shi ya kasance mai cin gashin kansa, dan haka da muguwar rawa gara kin tashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG