Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Da Chelsea Na Ra'ayin Zawarcin Dan Wasan Barcelona


A yayinda kungiyoyin kwallon Kafa na duniya suka fara zawarcin ‘yan wasan da zasu fafata masu a gasar lig lig ta kasashe daban daban a bana.

Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United zata biya yuro miliyan €140 kimanin fam miliyan £121 kan sayen dan wasan gefe na kungiyar Real Madrid mai suna Gareth Bale, mai shekaru 28 da haihuwa.

Har ila yau Manchester united, da takwararta Chelsea, duk kansu suna da ra'ayi wajan zawarcin dan wasan baya na gefen hagu daga kungiyar Barcelona, mai suna Jorda Alba, dan shekaru 29 a duniya.

Dan wasan gaba na Bayern Munich, Robert Lewandowski ya shaida wa mahukunta a kungiyar cewar yana da bukatar barin kulob din a karshen kakar wasan bana inda ake alakantashi da komawa kungiyar Chelsea, ko kuma Paris Saint-Germain, ko Real Madrid.

Kungiyar AS Roma, zata bukaci kudin da yakai yuro miliyan €90 kimanin fam miliyan £79 daga wajan kungiyar Liverpool, kan sayen mai tsaron ragarta Alisson dan shekaru 25 da haihuwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG