Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-Hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Riyad Mahrez

Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester City tana shirin kammala cinikin dan wasan gefe daga kulob din Leicester City, mai suna Riyad Mahrez, mai shekaru 27 da haihuwa akan kudi fam miliyan £75.

Liverpool ta kara kaimi wajan sayen dan wasan tsakiya kuma Kaftin a kungiyar Lyon, mai suna Nabil Fekir mai shekaru 24 a duniya bisa darajar kudi fam miliyan £60 wanda zasu fara tattaunawa a satin da za a shiga kan batun.

Manchester United, ta sa ido kan dan wasan tsakiya na kungiyar Aston Villa, mai suna Jack Grealish dan shekaru 22 a duniya, don ganin ta kawo shi kungiyarta.

Napoli ta yi watsi da tayin kudi fam miliyan £39 wanda kungiyar Manchester City, ta yi akan dan wasan tsakiyarta mai suna Jorginho, inda ta bukaci a biya ta fam miliyan £52 kan dan wasan dan kasar Itali.

Daraktan wasanni na kungiyar Kwallon Kafa ta AS Roma. ya ce babu wata kofa da zasu bayar kan mai tsaron ragarsu mai suna Alisson mai shekaru 25, wanda ake alakant ashi da komawa kungiyar Liverpool.

Domin karin bayani, saurari cikakken shirin a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG