Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Unai Emery Ya Maye Gurbin Arsene Wenger


.
.

Kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila ta bayyana sunan tsohon Kocin PSG Unai Emery, a matsayin Sabon kocinta wanda ya maye mata gurbin Arsene Wenger, wanda ya ajiye aikinsa da kungiyar a karshen kakar wasan bana bayan ya shafe shekaru ashirin da biyu yana jagorancin kungiyar.

Emery, mai shekaru 46 da haihuwa an tabbabtar masa da wannan matsayinne a ranar Laraba 23/5/2018 bayan sun samu daidatawa da mahukunta a kungiyar ta Arsenal, kafin zuwa ya kasance Kocin PSG inda a bana ya jagoranci kungiyar wadda ta lashe gasar Ligue 1 na kasar faransa da ma wasu kofuna

Emery, ya ajiye aikin sa ne kasancewar ya kammala yarjejeniyar kwantirakinsa da kungiyar PSG.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG