Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Muhimman Batutuwa Game Da Zinedine Zidane


Zinedine Zidane
Zinedine Zidane

Kocin kungiyar kwallon Kafa na Real Madrid Zinedine Zidane, ya ajiye aikinsa na mai horas da kungiyar. bayan ya lashe kofin zakarun turai kwanaki biyar da suka wuce.

Zidane mai shekaru 45 da haihuwa ya bayyana hakanne a ranar Alhamis 31/5/2018 a wani taro da ya kira na manema labarai. cikin taron harda shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez.

Zinedine Zidane, ya ce ya ajiye aikin ne saboda abin da ya ke tsammani shi ne cewa wannan kungiyar na bukatar ci gaba da samun nasara, don haka yana ganin ana bukatar canji, daban-daban, wannan shine dalilin da ya sa ya dauki wannan mataki.

Zidane, ya kama aiki da kungiyar Real Madrid, a watan janairun shekarar 2016, kimanin shekaru biyu da rabi da suka wuce bayan ta Sallami kocinta a lokacin Rafael Benitez.

Ya kuma jagoranci kungiyar a wasanni 149 inda yayi nasara a 104 kunnen doki 29 ya samu kashi 69.8 cikin dari a yayin zamansa a kungiyar inda ya lashe kofuna guda takwas a matsayin sa na mai horas wa, wanda suka hada da Kofin zakarun nahiyar turai sau (3) a Jere. World Club Cup (2) Super Cup (2) Laliga sau (1).

Daga karshe ya gode wa shugaban kungiyar ta Real Madrid. Perez da ya bashi dama ya buga wasa a kungiyar kuma ya zamo mai horas da ‘yan wasan kungiyar, ya kuma yaba wa ‘yan wasan kungiyar bisa hadin kai da suka bashi a yayinda yake wannan aiki har aka kai ga samu nasarori. Yace yana tare da kungiyar a duk inda yake.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG