Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Athletic Bilbao Ta Doke Barcelona A Copa Del Rey 2016/2017


A cigaba da wasannin Copa del rey zagaye na goma sha shida (Round of 16) na shekarar 2016/2017 a can kasar Spain jiya kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao ta doke takwararta ta Barcelona da ci 2-1

Za'a cigaba da wasannin karo na biyu cikin zagaye na goma sha shida ranar Talata 10/1/2017, inda Atletico Madrid zata kara da Las palmas.
A ranar laraba 11/1/2017 kuma kungiyar kwallon kafa ta Cordoba zasu fafata da Alcorcon.
Villarreal da Real Sociedad, sai Alaves da Deportivo. Barcelona zata karbi bakuncin Athletic Bilbao.

Ranar Alhamis 12/1/2017 kuma kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo, zata kece raini da Valencia, Eibar zata fafata tsakaninta da Osasuna, Sevilla zata karbi bakuncin Real Madrid.

A yau kuma za'a dawo fafatawa a bangaren La-liga 2016/2017 mako na sha bakwai

Esponyol zata gwabza da Deportivo
Da misalin karfe tara saura kwata agogon Najeriya Nijar kamaru da Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG