Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Firimiya Lig 2016/2017 Mako Na 20


A cigaba da fafatawa da akeyi a kasar Ingila bangaren firimiya lig na shekarar 2016/2017 an shiga mako na ashirin 2/1/2017, kungiyar kwallon kafa ta MiddleBrough ta yi canjaras 0-0 tsakaninta da Leicester City.

Manchester city ta sha Burnley 2-1

Sunderland ta yi 2-2 tsakaninta da Liverpool

Everton ta lallasa Southampton kwallo 3-0

Westbromwich ta doke Hull City da kwallaye 3-1

Westham tasha kashi a hannun Manchester United da kwallo 2-0.


A yau kuma za'a cigaba da Sauran wasannin kamar haka;
Kungiyar kwallon kafa ta AFC Bournemouth zata karbi bakuncin Arsenal

Stoke City zasu kece raini da Watford

Crystal palace zata kara da Swansea City

Za'a buga wasannin a lokuta daban daban agogon Najeriya Nijar kamaru da kasar Chadi
Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ke mataki na daya da maki 49, a wasa sha Tara da tayi.
Liverpool na mataki na Biyu da maki 43,
Manchester city tana mataki na Ukku da maki 42,

A kasan teburin kuwa
Sunderland na mataki na goma sha takwas da maki 15,
Hull City na mataki na goma sha tara da maki 13, Swansea, kuwa tana mataki na ashirin ne da maki12.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG