Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Firimiya Lig Mako Na 19


A ci gaba da fafatawa da akeyi a gasar firimiya lig, mako na ashirin a jiya kungiyar kwallon ta Middlebrough tayi canjaras da kungiyar Leicester City, inda suka tashi babu wanda ya jefa kwallo a raga.

Everton, kuwa ta sami nasarar doke Southampton ci ukku da daya yayinda Manchester City, ta sami nasara akan Burnley, da ci biyu da daya. Sunderland kuwa tayi kunnen doki biyu da biyu da Liverpool, yayinda West Bromwich, da lallasa Hull City, da ci ukku daya, West Ham, kuwa ta sha kashi a hannun Manchester United, da ci biyu da nema

A saman teburin firimiya lig, kuwa kungiyar Chelsea ke jan ragamar a wasanni goma sha tara da tayi inda take da maki arba’in da tara,Liverpool, tana mataki na biyu ne da maki araba’in da hudu,Manchester City, tana mataki na ukku, da maki arb’in da biyu.

A kasan teburi kuwa Sunderland, tana mataki na goma sha takwas da maki goma sha biyar yayinda Hull City, take mataki na goma sha tara da maki goma sha ukku, Swansea City, tana mataki na ashirin da maki goma sha biyu.

A yau za’a ci gaba da fafatawa a gasar firimiyar, inda kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, zata karbi bakuncin Arsenal, da misalign karfe tara agogon saura kwata agogon Najeriya,Nijar da Kamaru.

Crystal Palace zata kara da Swansea city, yayin da Stoke City, zata karbi bakuncin Watford.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:32 0:00

XS
SM
MD
LG