Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Marseilles Zata Kashe Fan Miliyan £30 Ko £40 Domin Dawo Da Dimitri Payet


A hada hadar saye da sayarda 'yan wasan kwallon kafa tn duniya da akeyi yanzu haka, kungirar kwallon kafa ta Real Madrid, ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £50 domin zawarcin dan wasan tsakiya na kasar Ingila mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham mai suna Dele Alli, dan shekara ashirin da haihuwa.

Ita kuma kungirar kwallon kafa ta Barcelona, ta ce ta fara tattaunawa da mai horas da kungirar kwallon kafa na Everton, mai suna Ronald Koeman, domin yuwuwar dawowarsa Kungiyar a matsayin mai horaswa inda ake saran zai maye gurbin Luis Enrique, a kakar wasan badi mai zuwa.

Chelsea na zawarcin dan wasan baya na gefe daga kungiyar kwallon kafa ta Juventus, mai suna Alex Sandro.

Marseilles, na kasar faransa na sha'awar dawowa da tsohon dan wasanta Dimitri Payet, zuwa kungiyar wanda a yanzu haka yake taka leda a kungirar Westham, Kungiyar ta ce domin ganin ta dawo dashi.zata kashe fam miliyan £30 ko £40
Maihoras da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya ce har yanzu ba'a cimma yarjejeniya game da sabunta kwantirakin dan wasanta mai suna Jack Wilshere, Wanda kwantirakinsa zai kare a shekara Mai kamawa ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG