Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester Na Iya Kai James Rodriguez Fam Miliyan £50


A Bangaren hada hadar 'yan wasan kwallon kafa na duniya
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, tana zawarcin dan wasan Real Madrid mai suna James Rodriguez, ana ganin Manchester zata iya kai shi fam miliyan £50, wajan sayen dan wasan

Har ila yau kungiyar ta Manchester united din na neman dan wasan gaba na Tottenham, mai suna Harry Kane, akan kudi fam miliyan £80.

Everton na zawarcin mai tsaron baya na Kungiyar Manchester United, Chris Smalling.

PSG, na shirin sayen Julian Draxler, dan shekara ashirin da ukku da haihuwa daga kungiyar kwallon kafa ta Wolfsburg.

Arsenal tace zata kara tsawaita kwantirakin dan wasanta mai suna Jack Wilshere dan shekaru Ashirin da biyar da haihuwa wanda kwantirakinsa zai kare a shekara mai zuwa.

Paul Clement ya amince da zamowa Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Swansea, na tsawon shekaru biyu masu zuwa inda zai maye gurbin tsohon kocinta Bob Bradley, wanda kungiyar ta kore shi a satin da ya wuce.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00

XS
SM
MD
LG