Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Lallasa Sevilla A Copa Del Rey 2016/2017 (Round 16)


A cigaba da wasannin da akeyi a can kasar Spain na Copa del rey 2016/2017, jiya an kece raini tsakanin kungiyoyi guda shida a matakin zagaye na Goma Sha shida (Round of sixteen) inda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta doke takwararta ta Sevilla da kwallaye 3-0.

Alcorcon ta yi canjaras 0-0 tsakaninta da Cordoba

Itama Real Sociedad, ta samu nasara akan Villarreal da ci 3-1

A yau kuma za'a kece raini tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao, da Barcelona, da misalin karfe tara da kwata agogon Najeriya Nijar Kamaru da Chadi.

Za'a kuma dawo zagaye na biyu a gasar ranar talata goma ga watan janairu na shekara ta dubu biyu da Goma Sha bakwai.

A bangaren firimiya lig 2016/2017, na kasar Ingila jiya Tottenham ta doke Chelsea da kwallaye 2-0.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG