Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zlatan Ya Zamo Gwarzon Dan Wasa (PFA Fan Premier League player of The Month)


A cigaba da akeyi na gasar firimiya lig 2016/2017 a kasar Ingila, Kungiyar magoya Bayan kwallon kafa bangaren firimiya lig ta zabi dan wasan gaba na Manchester United, Zaltan Ibrahimovic, a matsayin haziqin dan wasa na watan Disambar sheakarar 2016, da tawuce wato (Fan player of the Month) a bangaren firimiya lig na bana 2016/2017.

Zlatan, ya kasance gwarzon dancwasanne Sakamakon jagorantar kungiyarsa ta Manchester united, wajan samun nasara a wasanni shida a jere ba tare da an sha suba.

Dan wasan ya jefa kwallaye har guda biyar a wasanni shida, a yanzu haka Zlatan shine dan wasa na ukku acikin jerin Sunayen waydanda suka fi kowa jefa kwallo a gasar firmiya lig ta shekarar 2016/2017, Zlatan na da kwallaye Goma Sha Ukku a yanzu haka.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG