Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Shanghai Na Zawarcin Emerick Aubameyangn Akan £150 Da Albashin £800


A hada hadar kasuwanci na yan wasan kwallon kafa ta duniya
Kungiyar kwallon kafa ta Shanghai, ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £150 domin zawarcin dan wasan gaba na kasar Gabon mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, mai suna Emerick Aubameyang, inda zata dunga bashi fam dubu dari £800 a duk sati a matsayin albashi.

Ita kuwa kungirar Westham united tace tana so Sunderland ta fadi kudin da takeso domin sayar da dan wasan gabanta mai suna Jermain Defoe.

Juventus ta bukaci kungiyar Arsenal, da ta bata dan wasan gabanta mai suna Alex Sanchez ita kuma zata ba Arsenal dan wasanta Pjanic.

Everton na zawarcin dan wasan baya na tsakiya daga kungiyar kwallon kafa ta Southampton mai suna Ben Gibson.

MiddleBrough ta kammala sayen dan wasan Aston Villa mai suna Rudy Gestede akan kudi fam miliyan £6 na tsawon shekaru ukku masu zuwa a yanzu haka ya je kungiyar domin duba lafiyarsa kafin fara wasa a kulob din

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG