Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Na Adawa Da Mata Su Nemi Ilimi - Inji Ummulsalam Sunusi


Ummulsalam Sunusi
Ummulsalam Sunusi

Ummulsalam Sunusi wata matashiya mai karantar harshen Turanci da Hausa ta ce babban abinda ke ci mata tuwo a kwarya bai wuce yadda wasu daga cikin dangi ke korafi dangane da karantun gaba da sakandaren da take yi a yanzu.

Ta ce mafi yawanci wasu na ganin cewar aure shine babban abinda ya dace ga diya mace, kuma basa la’akari da irin cigaban da ake samu na rayuwa musammam ma a wannan lokaci.

Ummulsalam ta ce ta so ta karanci aikin likitanci amma bata samu nasara ba a jarrabawarta ta JAMB, gudun kada ta bata lokaci ta nemi gurbin karantar NCE .

Burinta dai bai wuci ta zama malamar makaranta ba, a cewarta malamai suke bada tarbiya ga al’umma, idan alumma ta yi kyau daga malami ne idan akasin haka ne ma daga gare su ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG