Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumai Mata A Bollywood Likkafa Tayi Gaba


deepika main
deepika main

Yanzu daga dukkan alamun ba maza bane kawai ke fina finai dake tattare da jarumtaka da hadari a Bollywood. Jarumai mata a Bollywood, suma sun fara nuna bajintarsu a wadannan fannoni, kuma sun yi amanna da wannan sabon fanni da suka fara dauka.

Kamar wanda Shraddha Kapoor ta dauka a fim din Baaghi, kuma gashi yanzu Deepika Padukone, itama a fim din “The Return of Xander Cage”.

Yanzu wandanna sune jaruman irin wadannan fina finai masu tattare da nuna bajinta na tunkarar hadarurruka a Bollywood.

Bugu da kari kuma akwai Sonakshi Sinha, kamar yadda itama ta ba marada kunya a fim din Akira, sailili nan kuma ga sabon fim dimta “ Force 2”. Sonakshi, a shirye take tayi fiye da abinda da tayi a fim din Akira.

Akwai fadace fadace, tseren motoci da harbe harbe da bindigogi duk a cikin wanna sabon fim din.

Da kuma aka tabayeta da wace mace take ganin cewa zasu yi wannan fim din tare batayi wani tantama ba ta anbaci sunnan Deepika.

Ta kara da cewa hatta fadar Kunfu, na Chinesse, shima ba’a barta a baya ba, tana da kwarewa akai.

Bayan ganin kadan daga ciki a fim din “ The Return Of Xander Cage” mun tabbatar cewa ta baiwa marada kunya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG