Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Sace Dan Abokinsa Mai Shekaru Biyar Domin Ya Sayarda Dashi A Abuja


Rundunar ‘yan Sandan jihar Benue, ta nuna wani manomi mai suna Unogwu Agbese, wanda ake zargi da laifin sace dan abokinsa mai shekaru biyar domin ya sayarda shi a Abuja.

Kakakin ‘yan Sandan jihar ASP Moses Yamu, yace maihaifin yaron ne ya kawo rahoton ga ‘yan Sanda, cewa abokinsa ya dauki dansa zuwa Abuja, batare da izini ba.

Kakakin ‘yan Sandan ya ce an cafke wanda ya sace yaro, kuma a samu yaro batare da an cutar dashi ba.

Ya kara da cewa a lokacin da ake masa tabayoyi Unogwu ya amsa laifinsa yana mai cewa ya dauki yaron ne domin ya sayarda shi a Abuja, amma Allah bai say a samu mai saye ba.

XS
SM
MD
LG