Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Damfari Wani Dan Sanda


Dan Sandan Najeriya.
Dan Sandan Najeriya.

Wani matashi Gideon Chubu, mai shekaru talatin da daya, wanda yayi Sojan gona a jihar Benue, ya damfari wani dan Sanda Naira dubu arba’in zai kwashe watani goma sha biyu, a gidan sarka.

An dai gurfanar da Chubu, a gaban kuliya ne ana tuhumarsa da laifin zambar da yin Sojan gona wanda ya sabawa sashe 326, na dokar manyan laifuffukan jihar Benue, na shekarar 2004.

Shi dai Gideon Chubu, ya yaudari dan Sandan ne cewa zai taimaka masa a dauki kaninsa a Soja, tunda yake tunda farko ya gayamashi cewa yana aikin ne a ofishin hafsan hafsoshin Sojojin Najeriya.

Mai shara’a Lilian Chuba, wace ta zartar da hukuncin tace kasancewar wannan shine laifinsa na farko, hukuncin zai sama ishara ga duk wani mai niyyar yin irin haka.

XS
SM
MD
LG