Shugaban Kampanin SpaceX, Elon Musk ya bayyana shirin yadda za'a yi tafiya zuwa duniyar wata da mars ta hanyar wata roka mai suna BFR. Ana iya daidaita rokar ta yadda za ta iya tafiya cikin duniyarmu inda za ta iya zuwa wurare da dama cikin minti 30 da ko ina a duniya cikin sa'a daya.