A Birnin Washington DC, daruruwan mutane sun yi tseren shekara-shekara sanye da takalma masu tsini da ake gudanarwa a talatar da ke gab da shagalin Halloween.
Duk da yadda wutar daji ta kone gidaje a jihar California wani mai raba wasiku bai fasa kai wasiku ba
Dattijai a Birnin Johannesburg suna yakar tsufa ta hanyar damben boxing da ke basu damar motsa jiki don rage radadin tsufa.
Zai iya girka duk irin abinci da mutum ke bukata ta hanyar ba shi umarni a manhajar wayar hannu.Idan kana kan hanyar zuwa gida kana iya kunnashi ta waya don ya fara girki kafin ka iso kuma babu wani hadari a ciki.Bugu da kari, har da yin wanke-wanke da gyara waje bayan girki.
Yayin da mahaukaciyar guguwar teku mai suna Ophelia ta ratsa ta yankin Wales da ke Burtaniya wasu sun fita kallo.
Tun daga lokacin ya hadu da masu wannan harkar har ma da yin baja kolin nunin zane-zanensa da ke bayyana ire-iren kalubalai da tsangwama da rashin kula a rayuwa. Yana da burin yin aure watarana da kuma haihuwa kuma yana fatan bude wajen zane-zane inda zai iya koyar da wasu yara masu nakasa.
Ma'aurata da dama sun halarci gasar shekara-shekara na tseren sabe da mata a wuya na karo na 18 da aka gudanar a Jihar Maine. Ma'aurata sun yi rige-rige ciken tabo da sauran abubuwa domin lashe gasar inda zakarun suka samu kyautar tafiya zuwa Kasar Finland, barasa da kuma kudade.
Ba da dadewa ba za a koma amfani da tasi marar matuki. Volocopter, wani tasi ne mai tashi kuma marar matuki wanda zai iya daukan mutane biyu. Kampanin da ya kera wannan tasin ya ce kowa zai iya amfani da shi cikin sauki idan ka nema zai zo daukeka kuma biya da arha.
Yi Lodin Kari..