Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jarumai Sun Dawo Harkar Fina Finai a Bollywood


A Bollywood ranar da ake jira tazo,a jiya aka nuna fim din Bajirao Mastani da Dilwale, inda kuma jama’a suka nunawa fina finan karamci suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin kallo.

A bangare guda jama’a na farin ciki da irin kimiyar wadannan fina finai inda kuma a daya bangaren kuwa jaruman fina finan kamar Ranveer Singh da Deepika Padukone sune suka shiga zukatan masu kallo.

Wasu kuwa yekuwa suke yi domin jarumai kamar Raj-Simra’aka Shah Rukh Khan, Kajol da Dilwale sun dawo harkar fina finai.

Wannan ya nuwa cewa Bollywood, sun natsu waje tsamo wadanda zasu fito a cikin fina finan su wanda haka ya tabbata a jiya.

Ranveer da Deepika, sun gabatar da wani nunin farko na wani fim inda jarumai da dama suka halarta.

Ranveer da Deepika sun karrama baki kamar yadda ya kamata inda suke raka su har zuwa ga motocinsu da kuma rungumar ban kwana.

Bajirao ya cancanci kauna kuma muna farin cikin cewa jama’a sun jidadin fim din, muna kuma yiwa duk wadanda suka san wannan fim ya tabbata godiya.

XS
SM
MD
LG