Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Kwalejin Kere-Kere Ta Jihar Kwara Sun Gudanar Da Zanga-Zanga


Da misalin karfe 8:00 am na safiyar yau Talata, dandazon daliban makarantar kimiya da koyon aiki ta jihar Kwara, "Kwara State Polytechnic" suka gudanar da wani zanga-zangar lumana ga hukumomin makarantar. Inda suka rufe titin Ilori zuwa Jabba. Hukumomin makarantar sun bayyanar da cewar duk dalibin da bai rijistar azuzuwan shi da kuma biyan kudin makaranta ba a kankari ba, za’a cishi tarar naira dubu goma 10,000.

Ana cikin hakan hukumar makarantar ta saurari kukan matasan da amincewa su rage kudin daga 10,000 zuwa naira dubu biyar 5,000. Kuma sun yi karin bayani cewar duk dalibin da ya riga ya biya 10,000 za’a maida mishi da 5,000. Hukumar makarantar sun tsayar da ranar 11 ga wannan watan a matsayin ranar karshen ta rigista.

A bangaren daliban kuwa sun bayyanar da cewar, mafi akasarin iyayen su basu samu albashin suba, balle su basu kudin da zasu rigista, hakan shi yasa basu samu damar biyan kudin ba. Don haka suna kara kira ga hukumomi a kowane mataki da su dubi irin hali na tattalin arziki da kasar ke ciki.

Sun yi kira kai tsaye ga gwamnan jihar, da cewar ya taimaka wajen ganin an basu agajin gaggawa. A karshe kuwa an roki matasan da cewar su kokarta wajen zaman lafiya da lumana.

XS
SM
MD
LG