Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kocin Golden Eaglets Na Cikin Wadanda Ka Iya Cin Lambar Yabon "CAF"


Hukumar dake kula da kwallon kafa ta Afirka, (CAF) ta sa sunan kocin din Golden Eaglets, Emmanuel Amuneke, a cikin jerin sunayen wadanda ka iya cin lambar yabo na kocin din da yafi bajinta a wannan shekaran.

An fidda sunayen ne a wani taron da hukumar ta gudanar jiya a Abuja.

Jerin Sunayen ‘yan kwallon da zasu fafata domin cin lambar dan wasan da yafi murza leda kuwa sun hada da Baye Ba, daga Mali, Etebo Oghenekaro, Najeriya,Mahmoud Abdelmonem,Eygpt da Zanedine Ferhat daga Algeria.

Kwallon mata ma ba’a bar su a baya domin ba Gabrielle Onguene da Gaelle Enganamoiut, ‘yan kasar Kamaru suma sun samu shiga Ngozi Ebere, daga Najeriya, Tia Ines daga Cote d’Ivoire, da Portia Boakye, daga kasar Ghana .

XS
SM
MD
LG