Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata, Zaku Iya Auren Saurayi Mara Ilimi Kuma Bai Aiki Ko Sana'a?


Kamar yadda muka ji ta bakin wasu samari da dama dangane da auren budurwa mara ilimi da aikin yi ko sana’a, yau kuma mun koma daya bangaren ne domin jin tabakin ‘yan matan, ya take ne ‘yan mata?

Hauwa’u Haruna daga gandun albasa jahar Kano ta bayyana mana ra’ayinta, inda ta ce gaskiya zai yi wuya a matsyinta na ‘ya mace ta yarda ta auri saurayi ko namijin da bashi da ilimi, ba sana’a ko aikin yi! Ta kara da cewa a nata ra’ayin idan ta yarda ta auri mara ilimi kuma ba aiki ko sana’a, da me zai ciyar da ita? Ta ce aikin yi da ilimi na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da yakamata ‘yan mata su yi la’akari da shi domin kuwa a nata hasashen, abin hannu shine gishirin zaman duniya.

Ita kuma Zuwairiya Hassan Sale cewa tayi, a nata ra’ayin saurayi ko bashi da ilimi ko sana’a zata iya auren sa muddun yana da ilimin addini domin aikin yi ko kudi duk ana iya samun su daga baya.

Matashiyar ta kara da cewa neman aljanna na daya daga cikin hujjujojin da zasu sa ta auri saurayi ko namijin da baida ilimi ko sana’a. tace idan har saurayi na kaunar budurwa to zai bada kokari wajen ganin cewa ya bi shawarar matarsa, dan haka ta ce duk wannan ba matsala ba ce.

Saurari cikakkiyar hirar a nan..dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG