Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gayyato Sabbin 'Yan Wasa a Super Eagles


'Yan Wasan Super Eagles
'Yan Wasan Super Eagles

Kocin Super Eagles Sunday Oliseh, ya gayyato Gbolahan Salami, Chima Akas da wasu ‘yan wasa 24, a wani yunkurin na shiri domin tukarar gasar cin kofin nahiyar Afirka da za’a buga a kasar Rwanda.

Kungiyar ta Super Eagles tana rukunin “C” a gasar tare da kasashen Niger, Tunisia da Guinea zasu kuma yi wasa ne a filin wasa na Nyamirambo a Kigali.

‘Yan wasa kama Kalu Orji, Austin Oboroakpo, Jamiu Alimi,Ifeanyi Mathew, Paul Onobi, Usman Mohammad, Bature Yaro, Ezekiel Bassey, Tunde Adeniji, Chisom ChikataraPrince Aggrey, Ikechukwu Ezenwa da Olufemi Thomas duk an gayyato su.

A gasar ta cin kofin nahiyar Afirka na shekarar data gabata Najeriya ce ta sami cin Tagulla.

XS
SM
MD
LG