Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaima Ka Dara


A yau mun sami labarin raha ne daga Tijjani Ado wanda aka fi sani da TJ ya kuma bamu labarin wani mutumi mai arziki da ba ya son jin rediyo, kwatsam sai tafiya ta taso masa ya kuma niki gari zai tafi garin Sambisa.

Wannan attaijiri ya kama hanyar sa zuwa Sambisa kenan sai yayi kicibus da sojoji a kan hanya suna caje masu tafiya, sai kuwa suka tambaye shi inda ya dosa sai gogan naka ya ce Sambisa zai je, dajin haka sai suka tambaye shi shin baka da labarin abinda ya ke faruwa a garin ne?.

Bude bakinsa ke da wuya sai cewa yayi aibashi da labari, sojojin nan suka sa shi tsallen kwado, da ya sha wahala bayan sun sake shi, sai mutumin ka ya garzaya kasuwa ya sayo radio ya sa a motar sa, kai harda ban daki kuma ya daura guda akan bishiyar da ke tsakar gidan sa......

Ku biyo mu domin jin wasu labaran masu ban dariya ….dandalinvoa.com

XS
SM
MD
LG