Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amaju Pinnick Ya Karyata Jita Jitar Dauko Sabon Koci


Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick, ya karyata wasu rahotanni da aka yada ta shafukan yada zumunta cewar hukumar na yunkurin dauko wani koci daban domin taimakawa kungiyar ‘yan wasan na super eagles.

Pinnick ya kara da cewa a maimakon haka, hukumar ta Najeriya ta amince dari bisa dari da aiyukan babban kocin ‘yan wasan na yanzu Sunday Oliseh ya ke yi, koda shike muna so ya goga kafada da manya manyan koc koc da ke turai.

Shugaban ya kara da cewa a yanzu haka hukumar ta amince kuma babban kocin yayi gagaruman ayyukan da ya cancanci a jinjina mai.

Amaju Pinnic ya ce, idan jefa kwallaye a raga ce matsalar to lallai ya kamata a kirkiro wasu sababbin dabarun yin hakan, idan dai hakan ya zama dole sai an hada kai da wasu koc koc kafin a iya samun nasara.

Ya kara da cewa, misali a wasan zakarun turai, kulob din Manchester United ne yafi kowanne kulob jefa kwallaye a ingila, tamkar Kulob din Bayern Munic da Basalona a jamus da spaniya.

Dan haka babu wata matsala idan Oliseh ya yi gogaiyya da manya manyan koc koc na turai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG