Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Eagles Nada Rauni Wajen Cin Kwallo


Shugaban hukumar kwallon kafa na Najeriya, Amaju Pinnick, ya hakikance cewa shawarar da hukumar ta yanke na daukar Sunday Oliseh, a matsayin Kocin Super Eagles yayi daidai.

Oliseh, ya maye gurbin Stephen Keshi, ne a watan Yuli, na wannan shekarar bayan da Stephen Keshi, ya sabawa yarjejeniyar daukar sa aiki.

A lokacinsa ne mai tsaron gida Vincent Enyeama da Emmanuel Emenike, suka furta cewa sun sagale takalminsu na kwallon kafa.

Shugaban na hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ya ce bamu yi kuskure ba wajen daukar Sunday Oliseh, saboda shi dan kwallon ne kuma dan Najeriya, kuma yana da kima a idon duniya a faggen wasan kwallon kafa.

Ya umarci ‘yan Najeriya dasu kara yin hakuri, ya kuma yi kira ga ‘yan wasan na Super Eagles, dasu ci gaba da murza leda kamar yadda ya kamata.

Ya ce akwai shiri na wasan sada zumunta da hukumar ta shirya da Cote d’Ivoire da kuma Italiya, Yana mai cewa yakamata kungiyar ta tashi tsaye wajen cin kwallaye, domin tana da rauni wajen jefa kwallo a raga.

XS
SM
MD
LG