Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yaya Samari Za Su Kauce Ma Matsalar Da Kan jawo Rabuwa Da Masoyan Su?


A shirin namu na yau, mun sami zantawa ne da wasu samari domin ra'ayin su akan matakai ko abubuwan da zasu kaucewa domin gudun samun matsala a tsakanin su da masoyan su wanda yawanci kan kaiga rabuwa.

Da muka ji ta bakin daya daga cikin matasan wanda ya bayyana ra'ayinsa inda ya ce a ganinsa karya ce ke haddasa yawancin matsala tsakanin samari matasa da masoyan su.

Wasu kuma daga cikin samarin sun nuna cewar baya ga karya , babban abinda ke jawo matsalar rabuwa tsakanin samari da masoyan su shine hanken kitsen da suke wa rogo, wato kwadayin duniya da sauran su.

Saurari cikakkiyar hirar a Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG