Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Cafke 'Yan Okada Takwas


Jami'an tsaron 'Yan sanda sun kama wasu 'yan kabu kabu su takwas, da kuma baburan hawa da dama garin Ughelli, sakamakon wata zanga zanaga da masu tuka ababen hawan suka yi domin nuna rashin amincewar su bisa karin kudin tikitin harajin da karamar humar ke amsa daga hannusu a kullum.

Zanga zangar wadda aka fara ranar litinin da ta gabata ta dauki wani sabon salo a yayin da masu zanga zanagar suka yi artabu da jami'an tsaron farin kaya da ake kira task force, wadanda sune ke karbar kudin tikitin daga hannun 'yan okadan da ke aiki a yankin.

Masu hawa okadan sun koma tafiyar kilmitoci a kasa zuwa gidajen su a yayin da 'yan okadan suka ki daukar duk wani fasinja.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya bayyanawa mujallar vanguard cewar hana umrnin hana zanga zangar ya fito ne daga ofishin kwamishinan 'yan sandan jahar.

Koda shike daya daga cikin masu zanga zangar ya bayyana ma mujallar cewa sun dadae da daina zanga zangar amma jami'an na taski force suka cigaba da tursasa masu a kusa da babban randa bawul din post office, sa'an nan 'yan sanda da 'yan banga kuma suka kama dayawa daga cikin su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG