Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kungiyar Asiri Sun Sake Wani Kisan


Wasu da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne a birnin Benin dake jihar Edo a Najeriya, sun harbe wani mutun mai suna Odion Egbegbe.

Odion, wanda yake birkila ne wadanda ake zargi da kisan nasa sun fidda shi daga gidansa ne sai suka harbe shi wanda daga bisani suka yanke masa kai.

Wannan shi karo na biyu da ake kisa mai nasaba da kungiyar asiri a birnin na Benin.

A mako biyu da ya gabata an kashewani mutun mai suna Bright, wanda aka fidda shi daga cikin shagonsa wanda ke kallon barikin ‘yan sanda dake Ogida, akakuma harbe shi

XS
SM
MD
LG