Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gargadi Daga Malama Lami Sumayya Murtala Da Malam Mustapha Yako Ga Matasa


Malama Lami Sumaiyya Murtala da Malam Mustapha Yako sun da bada shawarwari ga matasa samari da ‘yan mata dangane da irin kalubalen da duka bangarorin biyu ke fuskanta musamman a lokacin da suke shirin zabar abokan zama wato aure.

Da farko mun fara jin ta bakin malama Sumaiyya ne inda ta yi bayanin cewa ya kamata idan saurayi zai je neman aure yakamata ya yi la’akari da irin gidan da budurwar ta fito, domin gujewa rashin mutumci.

Malamar ta kara da cewa su kuma ‘yan mata su kai zuciya nesa su bar tunanin idan basu sami mazan da zasu aura da sauri ba, domin komi da lokacin sa.

Shi kuma malam Mustapha Yako ya yi kira ne ga duka bangarorin biyu da su rika yin la’akari da hali nigari, da nagarta da kuma bin addini, domin kuwa a cewar sa duk abinda aka gina ko kulla akan karya bazai taba dorewa ba.

Ga cikakkiyar hirar…Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG